A yi taka tsan-tsan da bunkasar Sojin China - Japan

Japan ta bayyana sauye-sauye kan harkokin tsaronta a yayinda take bunkasa dakarun ta da ke kudancin kasar, a dadai lokacinda sojojin China ke kara bunkassa.

Japan dai tana raba iyakar ruwa da China, kuma ta yi kira da kasashen duniya da su kara sa ido kuma su yi taka tsan-tsan da China, a yayinda sojinta ke kara bunkasa.

Japan za ta kara inganta kariyar makamanta masu linzami saboda fargaba daga kasar Koriya wadda ke da makaman linzami.

Majalisar zartarwar Japan ta amince da sabon tsarin inganta harkokin tsaro, wanda za'a gudanar na tsawon shekaru goma.

Japan dai na sauya tsarin tsaronta ne tare da yin la'akari da yadda wasu kasashe a nahiyar Afrika ke kara hobbasa wajen tara manyan makamai.