Nigeria ta janye karar da ta shigar akan Dick Cheney

Dick Cheney
Image caption Tsohon mataimakin shugaban Amurka

Hukumomi a Najeriya sun janye tuhumar da su ke yiwa tsohon mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney, da wasu jam'ian kamfanin Halliburton, akan bada cin hanci ga wasu jam'ian gwamnatin Nigeria.

Kakakin hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Mr Femi Babafemi nya ce an janye tuhumar da ake yiwa Mr Cheney ne da wasu shugabannin kamfanin Halliburton da na KBR bayan da aka cimma wata yarjejjeniya a wajen kotu, inda wadanda ake zargi suka amsa zasu biya diyya.

Rahotanni sun ce za'a biya Nigeria dola miliyan 250 a sakamakon wannan yarjjeniya da aka cimma.

Mahukunta a Nigeria sun ce tuhumar ta shafi wani abun kunya ne na bayar da cin hancin dollar miliyan 180 ga jami'an Nigeria a tsakanin shekarun 1995 zuwa 2005 domin samun wata kwangiya mai tsoka ta gina wani kamfanin iskar gas.

Lamarin ya faru ne a lokacin da Mr. Cheney ke shugabantar kamfanin na Halliburton.