Obama ya rattaba hannu kan dokar haraji

Shugaba Barack Obama
Image caption Shugaba Barack Obama na Amurka

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya sanya hannu a kan wata doka ta zaftare yawan harajin da 'yan kasar ke biya, wanda magabacinshi ya faro.

Wannnan doka dai ta shafi Amurkawa masu hannu da shuni.

Mista Obama ya amince da wannan doka ne domin shi ma ya samu amincewar 'yan jam'iyyar Republican dangane da wani shiri da yake yi na kara yawan alawus din da ake baiwa marasa aikin yi a kasar.

To sai dai 'yan jam’iyyar Democrat da dama na adawa da wannan yarjejeniyar.

Elijah Cummings dan jam’iyyar ta Democrat ne wanda ya kuma kada kuri'ar kin amincewa da dokar.

A cewarsa: “Mutane masu matsakaicin samu za su sake shiga cikin wahala, masu arziki kuma arzikinsu zai karu saboda wannan doka”.