Hari a kan bututan mai a Neja Delta

Wurin hakar mai
Image caption Jagoran rundunar JTF a yankin Neje Delta

Rahotanni daga jihar Delta a Najeriya, sun ce an kai wani hari kan bututan danyen mai mallakar kamfanonin hakar mai na Agip da Chevron, dake jihar a yankin Naija Delta mai arziki man fetur.

Wata kungiya ce mai ikirarin kare 'yancin yankin Naija Delta, mai suna Niger Delta Liberation Force, (NDLF), ta ce ita ce ta kai wannan harin ranar Asabar.

Kawo yanzu dai babu ko daya daga cikin Kamfanoni da aka yiwa ta'adin da ya ce uffan.

Kakakin rundunar tabbatar da tsaro a yankin laftanar kanar Timothy Antiga ya shaida wa BBC cewa sun samu labarin abkuwar haka, amma ba su da tabbaci a kan haka.