Ba ma bukatar dakarun kasashen waje-Gbagbo

Sojojin 'yan tawaye
Image caption Sojojin da ke marawa Alhassan Quatara baya na tattaunawa

Laurent Gbagbo, wanda ke fuskantar matsin lamba na ya sauka daga kan mulkin kasar Ivory Coast, ya bukaci dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD da na Faransa da su fice daga kasar ba tare da bata lokaci ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, an budewa dakarunta dake sintiri wuta a lokacin da suka shiga harabarsu dake birnin Abidjan.

Kakakin gwamnatin ta Cote d'Ivoire, Jacqueline Oble, ta zargi rundunar kiyaye zaman lafiyar majalisar dinkin duniya da tada zaune tsaye a kasar, tare da taimakawa wajen rarraba kawunan jama'ar kasar:

Ta ce: "Gwamnatin Cote d'Ivoire na ganin cewa, majalisar dinkin duniya ta nuna gazawa sosai, yayin da take yin wasu aikace-aikacen da suka sabawa ka'idojin aikinta a kasar.

Shugaban kasa, Laurent Gbagbo, ya bukaci ma'aikatan kiyaye zaman lafiyar majalisar da su bar Cote d'Ivoire nan take, tare da dakarun Faransa da ke rufa masu baya.

An cigaba da samun zaman dar-dar a Cote d'Ivoire din, tun bayan da shugaban tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar, Young Jin Choi, ya fito fili ya bayyana cewa, jagoran 'yan adawa ne, Allasane Ouattara, ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamban da ya wuce.

Wata yarjajeniyar kawo zaman lafiyar da dukkan bangarorin suka sawa hannu, ita ce ta ba Majalisar Dinkin Duniya izinin rattaba hannu a sakamakon zaben.