PDP zata yi zaben fidda gwani na gwamnoni

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Jamiyyar PDP mai mulki a Najeriya ta ce, ba zai yiwu a baiwa gwamnonin jihohin da ta ke mulki tikitin tsayawa takara kai tsaye, ba tare da an gudanar da zaben fidda gwani ba .

A cewa jam'iyyar, hakan ya sabawa dokokin kundin tsarin mulkinta, da kuma tsarin demokradiyya.

A baya baya nan ne wasu rahotanni suka ambato shugaban kasar, Dr Goodluck Jonathan, dan jam'iyyar PDP yana cewa, za a baiwa gwamnonin jihohin jam'iyyar da suka cancanta, tikinti tsayawa takara kai tsaye.

Uwar jam'iyyar dai ta musanta hakan.

Galibin gwamnonin PDP sun kawo goyon bayansu ga takarar shugaba Goodluck Jonathan, a zaben da za a gudanar a Najeriyar a shekara mai zuwa.