'Ba inda sojojin Majalisar Dinkin Duniya za su'

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon
Image caption Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya yi watsi da bukatar Laurent Gbagbo ta dakarun kasa-da-kasa su fice daga Ivory Coast ba tare da bata lokaci ba.

Wata mai magana da yawun Mista Gbagbo ce dai ta bukaci dakarun su fice daga kasar, tana zarginsu da hada baki da tsofaffin 'yan tawaye.

Majalisar Dinkin Duniyar da Mista Gbagbo sun tasamma sa kafar wando guda.

Mista Gbagbo dai ya kekasa kasa ya ki sauka daga kan kujerar shugabancin kasar ta Ivory Coast, sannan ya bukaci dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya su san inda dare ya yi musu.

To amma Mista Ban ya ce wannan bukata ba za ta sabu ba, sannan ya yi gargadin za a dauki mataki a kan duk wani hari da za a kaiwa dakarun na Majalisar Dinkin Duniya.

A cewar Babban Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya, bakin daukacin kasashen nahiyar Afirka ya zo daya a kan cewa abokin adawar Mista Gbagbo, wato Alassane Ouattara, shi ne ya lashe zaben da ake takaddama a kansa.

Sai dai matsalolin Majalisar ta Dinkin Duniya sai karuwa suke yi: yayinda wa'adin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar ke karewa a karshen wannan watan, Mista Ouattara kuma ke ci gaba da zama a wani otal, har yanzu babu wani daga cikin magoya bayan Mista Gbagbo da ya nuna alamun zai sauya sheka.

Karin bayani