Amurka ta halalta daukar 'yan luwadi soja

Shugaba Barack Obama na Amurka
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Majalisar Dattawa ta Amurka ta dage haramcin daukar 'yan luwadi da madugo aikin soja.

'Yan Majalisar sun kada kuri'ar soke dokar, wadda ta ke tilastawa 'yan luwadi da madugo boye halayyar tasu ko kuma a koresu daga aikin soja.

Dokar dai ta jawo rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan jam'iyyar Democrat da 'yan jam'iyyar Republican a Majalisar.

Daga karshe dai sai da wadansu 'yan jam'iyyar Republican din suka marawa takwarorinsu 'yan Democrat baya kafin su samu damar kawo karshen dokar wadda aka yi shekaru goma sha bakwai ana aiwatar da ita.

Wannan shawara ta soke dokar wata babbar nasara ce ga Shugaba Obama wanda ya yi alkawarin kawar da ita lokacin da yake yakin neman zabe.

Shugaban na Amurka ya yi marhabin da wannan mataki, yana mai cewa daga yanzu ba sai Amurkawa masu kishin kasa sun yi karya ba kafin su samu damar yiwa kasarsu hidima.

Fiye da sojoji dubu goma sha uku ne dai aka sallama tun bayan fara aiki da dokar a shekarar 1993.

Sai dai masu goyon bayan dokar haramcin sun ce dage ta a lokacin yaki zai kassara karfin gwiwar sojojin kasar.