'Tarrayar Turai za ta dakatar da Laurent Gbagbo'

Image caption Laurent Gbagbo

Tarrayar Turai ta amince da dakatar da shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo, bayan ya ki amicewar da kayin da aka yi masa a zaben shugaban kasar.

Shugaban kasar Faransa Nicholas Sarkozy ya baiwa Mista Gbagbo wa'adin ranar Lahadi domin ya sauka daga kan mulki.

Mista Gbagbo da Alassane Ouattara ne suka yi takara a zaben a yayinda kowannensu ke ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben.

Kowannensu dai ya fito da jerin sunayen ministocinda za su yi aiki da su, a yayinda ake ci gaba da zaman fargaba a birnin Abidjan babban birnin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar ECOWAS da na tarrayar Afrika dai sun baiwa Mista Ouattara goyon baya, a yayinda suka ce shi ne ya lashe zaben.

Wani jami'in diplomasiyya ya shaida wa BBC cewa, tarrayar Turai, ta dau matakin dakatar da Mista Gbagbo da jami'an gwamnatinsa 18.

Jami'in ya ce shugabanni tarrayar za su amince da matakin nan da kwanaki biyu ko guda.