Magoya bayan Gbagbo na ta da tsimin matasa

Mista Laurent Gabgbo na Ivory Coast
Image caption Mista Laurent Gabgbo na Ivory Coast

Har yanzu kasar Ivory Coast na fuskantar turka-turkar siyasa, inda shugaba mai ci, Laurent Gbagbo, ya ki ajiye mukaminsa—duk kuwa da matsin lambar kasashen duniya—ya kuma umurci dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar su tattara nasu-ya-nasu su bar kasar.

Mista Gbagbo ya zargi dakarun kiyaye zaman lafiyar ne da goyon bayan abokin adawansa, Alassane Ouattara, wanda ake kyautata zaton shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Yayinda ake ci gaba da zaman dar-dar a cibiyar kasuwancin kasar, Abidjan, a kullum jagoran kungiyar matasa masu goyon bayan Laurent Gbagbo sai gudanar da gangami ya ke a unguwannin birnin.

A wurin daya daga cikin wadannan tarukan gangami, dubban mutane ne suka yi ta ihu suna cewa “Majalisar Dinkin Duniya ta fice”, yayinda jagoran kungiyar Young Patriots—kungiyar da ke da muhimmanci ga goyon bayan da Laurent Gabgbo ya ke samu a tsakanin matasa—ya iso wurin taron.

Charles Ble Goude ya je wurin ne a saman wata bakar mota kirar Jeep wadda wasu mutanen da suka rufe fuskokinsu dauke da manyan makamai ke yiwa rakiya.

Ko da ya ke mutum ne mai dan karamin jiki, Charles Ble Goude yana da kwarjini; sai dai tun shekarar 2004 aka zarge shi da kitsa tashe-tashen hankula, Majalisar Dinkin Duniya kuma ta kakaba mishi takunkumi.

Charles Ble Goude dai ya san yadda zai ja hankalin gungun mutane.

A jawabin da ya yi ga taron gangamin da nufin zaburar da magoya bayan Laurent Gbagbo, ya zargi Shugaba Nicholas Sarkozy na kasar Faransa da Majalisar Dinkin Duniya da yin sanadiyyar kikikakar siyasar da kasar ta Ivory Coast ta fada.

Ya kuma shaidawa 'yan bindigarsa su zauna cikin shiri to amma kar su afkawa Faransawan da ke zaune a kasar ta Ivory Coast saboda, a cewarsa, ba su ba ne matsalar gwamnatinsu ce.

A bayyane ta ke dai cewa manufar wadannan tarurrukan gangami na Charles Ble Goude ita ce tabbatar da cewa 'yan bindigar a shirye su ke su marawa Mista Gbagbo baya a ko wanne hali.

Karin bayani