Gwamnonin PDP sun jaddada matsayinsu

Tambarin jam'iyyar PDP
Image caption Tambarin jam'iyyar PDP

Gwamnonin jam’iyyar PDP mai mulki a Najeriya sun ce suna nan a kan bakansu na marawa Shugaba Goodluck Jonathan baya a zaben fidda gwani na jam'iyyar, kamar yadda suka dau alkawari a taron Majalisar Zartarwar jam'iyyar.

A karshen makon jiya ne dai Shugaba Goodluck Jonathan da mataimakinsa, Architect Namadi Sambo, suka gana da dukkanin gwamnonin jam'iyyar ta PDP na shiyyar arewa maso yamma, tare da wasu shugabannin jam'iyyar na yankin a Kaduna, inda gwamnonin suka jaddada matsayinsu.

Gwamna Sule Lamido na Jihar Jigawa ya shaidawa wakilin BBC cewa:

“A tarbiyyar siyasa duk duniya, ko menene yanayin abin da ya faru a kasa, babu inda aka taba zuwa aka ce jam’iyya ta ka da shugabanta na kasa.

“Idan ta yi haka, ta gayawa mutanen Najeriya cewa ‘mu ‘yan PDP mutumin nan da muka zaba yau mun karya shi'”.

Da aka tambaye shi dangane da batun jajircewarsu ta tsayar da dan takara daga arewa kuwa, sai Gwamna Lamido ya ce in haka ne, kamata ya yi duk 'yan arewa su taru a bayan mutum daya; “amma ko haka din ne ba za mu sa wanda ya yakemu shekaru uku baya [ba]”.

“Ka gane, babu yadda za a yi wani yanayi na firgita mutane ko na tsoratarwa [wanda zai] firgita mu, [bayan] mun ci zabe shekaru uku baya, don tsabar wauta mu...ce mu ‘yan PDP wannan gwamnati mun karya ta; ba zai yiwu ba!”

Karin bayani