Dusar kankara na ci gaba da kawo cikas ga harkokin tafiye-tafiye

Image caption Jiragen sama da dama sun kasa tashi, saboda dusar kankara

Dubban mutane ne ke fuskantar rashin tabbas na yin tafiya a hutun Krismeti a Ingila, saboda yanayin dusar kankara da ta dabaibaiye kasar.

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na British Airways na fatan jirage 60 za su tashi a filin saukar jiragen sama na Heathrow, amma akwai jirage da dama da aka dakatar.

Kamfanin British Airways ya baiwa fasinjojinsa hakuri a yayinda suke ci gaba da kwana a dakin hutawa a filin saukar jiragen saman.

Sakatare kula da harkar sufuri na Burtaniya, Philip Hammond ya ce, dole ne a baiwa fasinjojin fifiko, saboda kare lafiyarsu na da matukkar mahimmanci.

An rasa rai

Wani mutum ya mutu asibiti, bayan da ya fadi a cikin kankara a kogin Essex.

Mutumin, wanda ke sahun shekaru talatin a duniya ya mutu ne kusa da Southend a ranar Lahadi.

Harwa yau, Ofishin nazarin yanayi ya yi gargadin cewar za'a kara samun dusar kankara a wurare da dama a fadin Burtaniya.

Kudancin Ingila da kuma Wales na cikin wuraren da ake ganin sanyin zai tsananta.

Motocin bada agajin lafiya na gaggawa sun yi gargadin cewar ba za su rika samun zuwa akan lokaci ba, idan aka neme su, saboda dusar kankara.

Mutane na cikin halin kunci

Dubban mutane ne suka kwana a filin saukar jiragen sama na Heathrow saboda jiragen da aka dakatar a ranar Lahadi.

Image caption Fasinjoji na cikin halin kunci a filin jirgin sama na Heathrow

Harwa yau dai hukumomin kamfanin jirgin sama na British Airways sun ce babu makawa sai an soke tashin wasu jiragen a filin saukar jiragen sama na Heathrow.

Amma fasinjoji da dama suna kara nuna rashin jin dadinsu kan yadda suke fuskantar matsaloli saboda rashin samun jiragen sama.

Sarah Randall daga Hertfordshire, ta ce tana filin jirgin saman ne tare da maigidanta da yaranta uku, bayan an dakatar da jirgin Cathay Pacific, wanda ya kamata ya kai su Hong Kong.

Ta ce ta kwana ne a kasa ranar Asabar, kuma har yanzu jikinta na yi mata ciwo, saboda bata taba yin hakan ba.

Ta yi korafin cewa: "Gaskiya muna fuskantar matsanancin sanyi, kuma muna cikin bakin ciki saboda yadda ake wulakantamu a filin jirgin sama".

Ta ce iyalanta sun koma gida, kuma har yanzu ba ta san ko za'a mayar musu da fam 16,000 da suka kashe na siyan tikiti ba.

Hukumomi na iyakacin kokarin su

Sakataren kula da harkar sufuri Mista Hammond ya ce ba shi da masaniya game da halin da fasinjoji su ke ciki, amma ya ce tsarin hakar sufurin kasar ya bada fifiko ga yadda za'a kare lafiyar matafiya.

Mai magana da yawun British Airways, Andrew Teacher ya shaida wa BBC cewar: " Muna yin duk mai yiwuwa domin kula da lafiyar matafiya, a yayinda muka samarwa wasu wajen kwana a wani Otel din da ke kusa da filin jirgin saman."

Mista Teacher ya kara da cewa: "Ba wai muna gudun sauke nauyin da ke wuyan mu bane, filin saukar jiragen sama na Heathrow ba daya ya ke da na Finland ko Istanbul ba. Muna da wurin jirage sama da dari biyu, kuma ga dusar kankara ta mamaye ko'ina, dole ne a fuskanci matsala."

Wakiliyar BBC a Heathrown Asha Tanna, ta ce: "Shugabannin kamfanoni jiragen sama na tattaunawa, domin ganin yadda za su rika jigilar matafiyan, muddin dusar kankarar ta sassauta.