Kotu ta wanke Manjo Al Mustapha

Image caption Manjo Hamza Al-Mustapha zai ci gaba da amsa tuhuma akan kisan Kudirat Abiola a wata Kotu a Lagos

Wata babbar kotun tarraya a Lagos ta wanke, babban dogarin marigayi janar Sani Abacha, wato Manjo Al Mustapha daga zargin yinkurin kisan mawallafin jaridar Guardian wato Alex Ibru da tsohon kwamishinan wasanni na jihar Delta Isaac Obeni.

Har yau kotun ta wanke Jibril Bala Yakubu da James Danbaba da kuma Mohammed Rabo Lawal wadanda ake zarge su tare da Al-Mustapha wajen yinkuri kashe mista Ibru.

A yanzu haka dai kotun ta saki CSP James Danbaba da kuma Kanal Jibril Yakubu, saboda babu wata tuhuma da za su amsa.

Kotu dai ta yi watsi ne da karar saboda ta ce babu wata kwakkwarar shaida da aka bayar game da zargin da akewa su Al-Mustapha, saboda haka ta wanke su daga zargin.

A yanzu haka dai Manjo Hamza Al Mustapha zai ci gaba da amsa tuhuma kan batun zarginsa da akeyi na kisan Kudirat Abiola a wata kotu a Lagos.