Bam ya halaka mutane uku a Kenya

Taswirar kasar Kenya
Image caption Bam ya fashe a Kenya

Bam ya fashe a tashar motoci da ke tsakiyar birnin Nairobi na kasar kenya, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku, inda fiye da mutane arba'in suka samu raunuka.

Rundunar 'yansandan kasar ta ce cikin mutanen da suka mutu, har da mutumin da ya rike jakar da ta fashe a lokacin da jami'an tsaro ke gudanar da bincike kan kayayyakin matafiya, da zasu shiga bus din da ke kan hanyar ta zuwa kasar Uganda.

Wani fasinja da ke cikin bus din ya ce mutane sun rude bayan da abin ya fashe.

Jami'an tsaro sun ce suna gudanar da bincike kan lamarin.