An kafa sabuwar gwamnati a Iraqi

Image caption Pira Minista Nouri Al-Maliki

Majalisar dokokin Iraqi, ta amince da kafa sabuwar gwamnati, lamarin da ya kawo karshen kiki-kakar siyasar da aka kwashe sama da watanni tara a na ciki a kasar. A wani zama na musamman da akai a majalisar dokikin, daya bayan daya 'yan majalisar sun kada kuri'a kan sunayen ministocin da Pira Minista Nouri al-Maliki ya zaba. Ba'a kafa gwamnati a kasar ba tun bayan zaben da akai a watan Maris, da jam'iyyu daban daban ke ta takkadama a kansa.

A makon da ya gaba ne aka kawo karshen takaddamar bayan da aka cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin guiwa,inda aka amince a ba Mr. Maliki damar sake rike matsayin Fira ministan karo na biyu.