Kungiyar Amnesty ta ce fararen hula na bukatar kariya a Coted'Ivoire

Image caption Laurent Gbagbo

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce fararen hula wadanda ba sa dauke da makamai na bukatar kariya ta gaggawa a kasar Cote d'Ivoire.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar , ta ce ta samu bayanan cewa sojoji da 'yan tada kayar baya dake dauke da makamai dake goyon bayan Laurent Gbagbo na kama mutane.

Kungiyar ta kara da cewa ana tsintar gawawwakin mutanen da aka sacen a wuraren ajiye matattatu na asubiti ko kuma a kan tituna, yayinda kawo yanzu ba a san inda wasu suke ba.

Tun farko mai magana da yawun Alassane Ouattaran, mutumin da ake ganin shi ya lashe zaben shugaban kasar na Ivory Coast, yayi kira ga dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da su kawar da shugaban kasar mai ci Laurent Gbagbo daga kan karagar mulki.

Mr Patrick Achi ya bayyana hakan, yana mai cewa matakin shi zai kawo karshen zub-da-jini, yayinda jayayyar neman iko ke ci gaba.

Suma dai Shugabannin kungiyar habbaka tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO sun yi kira ga Laurent Gbagbo ya mika mulki cikin martaba ba tare da bata lokaci ba.

Wata sanarwa da ECOWAS ta fitar yau dinnan ta kuma gargadi Laurent Gbagbo akan cewar ya daina fito na fito da dakarun samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake kasar.

Sai dai kuma gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta ci gaba da bin duk hanyoyin da suka kamata wajen ganin an kawo karshen rikicin siyasar daya barke a Ivory Coast, biyo bayan zaben shugaban kasar da ake ta takaddama akai.

Gwamnatin Najeriyar ta kuma ce rikicin siyasar Ivory Coast tamkar darasi ne ga sauran kasashen dake Nahiyar Afrika.

Ministan harkokin wajen Najeriya Dr. Aliyu Idi Hong , ya shaidawa BBC cewa shugaban da Nigeria ta sani a Ivory Coast shi ne Allasane Ouattara