Mawakan Najeriya suna amshin shata ne?

Image caption Marigayi Fela Kuti

A yayinda Najeriya ke shirin tunkarar zabuka a shekarar 2011, 'yan takara da dama suna ci gaba da kashe makudan kudade domin buga fastoci da sanya tallar kamfen dinsu a radio da kuma talbijin.

Wannan ne kuma ya sa wasunsu da dama, ke amfani da mawaka wajen rera wakokin kamfen din su.

Wasu fitattun mawakan turanci da hausa, kamar su D'banj da Onyenka Onwenu da Zaaki Azzay da TwoShotz da kuma wasu da dama sun rera wakar kamfe wa Shugaba Goodluck Jonathan, yayinda wasu suka rera wa abokan adawar sa nasu wakokin.

Amma ba kowa bane ke rawa

Seun Kuti dan shahararren mawakin nan da ya rasu Fela Kuti, ya ce abin kunya ne mawaka a kasar suna rera wa 'yan siyasa waka. "Duk mawakin da ya ke amfani da wakarsa wajen nemar wa dan siyasa goyon baya ya ci amanar kasa, da kuma ita kanta sana'ar waka." In ji Kuti.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A yayinda ake sama da fadi da biliyoyin nairori a kasar, sama da kashi 70 cikin dari na al'ummar kasar ne ke fama da talauci, a yayinda suke rayuwa a kan kasa da dalar Amurka daya a rana.

Tun da aka koma mulkin demoradiyya a kasar a shekarar 1999, Jam'iyyar PDP ce ke mulkin kasar, wadda kuma ake zarginta da murde zabuka da karfin tuwo.

Za a yi zaben shugaban kasa ne a ranar 9 ga watan Afrilu na shekarar 2011 a yayinda kamfe ya yi nisa

"Waka na daya daga cikin abubuwan da za a iya amfani da su domin fadakar da jama'a domin sanin 'yancinsu." In ji Kuti.

"Bai daceba, yadda ake amfani da ita wajen neman goyon bayan jama'ar da aka dade ana cuta." Masana na ganin matasa da dama ba sa fitowa domin kada kuri'a a lokacin zabe, amma ana ganin tunda suna matukar son wadannan mawaka, za su iya sama musu goyon baya."

Mawakan baya

A zamanin marigayi Fela Kuti - maihaifin Seun Kuti- ya rera wakoki ne da suka kalubalanci mulkin soji a lokacin da sauran 'yan siyasa, inda kuma ya yi ta fuskantar mastin lamba.

Olubankole Wellington - wanda aka fi sani da Banky W, na daya daga cikin shahararrun mawakan turanci a Najeriya, ya ce; " Akwai dan takarar da ya bani makudan kudade, wanda ban taba ganin irinsu ba domin in rera masa waka, amma saboda ban amince da shi ba, kin karba na yi."

"Ba zan iya barci ba, har idan na bashi goyon baya,"

"Ya kamata ne ace muna wayar da kan mutane domin su zabi wadanda za su kyautata rayuwar su, bai wai mu nuna goyon baya ga wani dan takara ba"

Yawancin mawakan dai sun ki su bayyana adadin kudaden da aka biya su domin rera wa 'yan siyasa waka.

Ya waka za ta taimaka wajen zabe

Manajan TwoShotz ya shaida wa BBC cewar, mawakin ya rera wakoki domin ya fadakar da 'yan Najeriya game da zabinsu.

"Muna fatan wakar za ta taimaka wajen ba mutane kwarin gwiwa domin su fito su kada kuri'a.

Wani mawakin, Zaaki Azzay, wanda ya rera wa shugaba Jonathan waka, ya ce bai karbi ko kobo ba kafin ya yi wakar.

Image caption Wasu mawaka a Najeriya

"Ba maganar kudi ba ce. Ina goyon bayan Mista Jonathan saboda sauye sauyen da ya fito da su, kuma ina da kwarin gwiwa zai kai kasar ga gaci."

Yawancin kamfe din Shugaba Goodluck Jonathan ya karkata ne ga matasa, domin ana ganin su suka fi yawa a al'ummar Najeriya.

A baya ma dai an yi irin wannan gangamin shekaru goma da suka wuce, inda marigayi Janar Sani Abacha ya yi amfani da mawaka da masu shirya finafinai, domin nema masa goyon baya.

Yanzu ta bayyana cewa 'yan siyasa, sun san irin goyon bayan da za su samu daga matasa, kuma suna kokarin amfani ne da mawaka domin cimma burinsu.

Amma abun tambaya a nan shi ne, ko waka mai dadi za ta sauya yadda matasan kasar za su kada