Dokar ta-baci a Thailand

Taswirar kasar Thailand
Image caption Za a dage dokar ta-baci a Thailand

Hukomomin kasar Thailand sun ce ranar laraba za'a dage dokar ta-bacin da aka sanya a birnin Bangkok fiye da watanni takwas da suka gabata.

Dokar dai ta baiwa jami'an tsaron kasar karfi na musaman, wanda ya hada da ikon tsare mutanen da ake zargi da aikata ba dai-dai ba har tsawon kwanaki talati ba tare an gurfanar da su a gaban kuliya ba.

An dai sanya dokar ne lokacin da aka gudanar da zanga- zangar nuna rashin amincewa da gwamnatin kasar a farkon bana, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye casa'in.

Rundunar sojin kasar dai ta nuna amincewarta da dage dokar ta-bacin.