Zaben shugabannin jam'iyyar CPC

Janar Muhammadu Buhari da ke son yin takara a jam'iyyar CPC
Image caption Za sake gudanar da zabe a jam'iyyar CPC

A yau laraba ne jam'iyyar adawa ta CPC da ke Najeriya za ta sake gudanar da zaben shugabanninta a matakin mazabu a wasu jihohi.

Jami'yyar ta soke zabukan da ta gudanar a jihohin Kano, da Kebbi, da Katsina a farkon watan da muke ciki, sakamakon korafe-korafen da wasu 'ya'yanta suka yi cewa ba a yi musu adalci ba.

Sai dai yanzu jam'iyyar ta ce za ta tabbatar an gudanar da zaben cikin adalci yadda ba za a yi korafi ba.

Sanata Rufa'i Hanga shi ne shugaban jam'iyyar na kasa, ya shaidawa BBC cewa wadanda suka yanki katin jam'iyya ne kawai za su kada kuri'a lokacin zaben, saboda a tabbatar da adalci.

Ya yi zargin cewa wasu 'yan takara sun yi hayar 'yan daba don ganin ba a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali ba, sai dai ya ce a shirye jam'ian tsaro suke wajen tabbatar da doka a lokacin gudanar da zaben.