Yajin aikin ma'aikatan sufuri ya tsayar da kome a Girka

Wani yajin aikin da ma'aikatan sufuri ke yi a kasar Girka ya tsaida harkoki cik, a Athens, babban birnin kasar.

Wakilin BBC yace, Jama'a na amfani da motocinsu wajen zuwa aiki dan haka akwai cunkosan ababen hawa a hanyoyin shiga tsakiyar birnin Athens.

An shirya yajin aikin ne don ya zo daidai lokacin da za a kada wata kuri'a a majalisar dokokin kasar, akan kasafin kudin shekara mai kamawa, ta 2011, kasafin da gwamnati ta shirya tsuke bakin aljihunta.

Ana sanya ran gwamnatin za ta samu nasarar amincewa da kasafin kudin, wanda aka shirya shi domin ya gamsar da hukumar bada lamuni ta duniya, IMF, da kuma tarayyar turai, a matsayin wani sharadi na baiwa kasar ta Girka lamunin dola biliyan 145.