An dakatar da ba Ivory Coast bashi

'Yan kasar Ivory Coast
Image caption Shugaba Nikolas Sarkozy na Faransa ya gana da shugaban bankin duniya kan kasar Ivory Coast

Babban bankin duniya ya dakatar da duk wata huldar kudi da Ivory Coast, yayin da ake ci gaba da takaddamar siyasa tsakanin Alassane Ouattara, wanda kasashen duniya ke dauka a matsayin shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da akai, da kuma Laurent Gbagbo dake kan mulki.

Shugaban bankin duniyar, Robert Zoellick, yace an dakatar da ba kasar bashi, bayan tattaunawar da sukai da shugaban Faransa Nikolas Sarkozy.

Yanzu haka kasashen Faransa da Jamus sun ba yan kasarsu dake Ivory Coast shawara na su bar kasar.

A waje daya kuma gwamnatin Laurent Gbagbon ta aika wata tawagar jami'anta biyu zuwa Kamaru domin su bayyana wa Gwamnatin Shugaba Paul Biya, tare da alummomin Kamaru abinda suka ce shi ne gaskiyar abinda ya wakana bayan zaben shugaban kasar da ya haifar da wannan rudani.