Zaben Jama'iyar CPC ya faskara a Kano

A Nigeria an sake dage zabukan unguwanni na jam'iyyar CPC a jahar Kano.

Wannan dai shi ne karo na biyu cikin kasa da makwanni biyu da aka dage zabukan bayan soke na farko da aka yi, wanda aka gudanar ranar 11 ga wannan watan.

Tun farko dai an tsayar da ranar asabar ta makon jiya a matsayin ranar da za a gudanar da zabukan kafin daga baya a daga zuwa yau.

Hakan dai ya biyo bayan rigingimun da jam'iyyar take fama da su.

Shugaban Jama'iyar a jihar Kano ya ce an dage zaben na yau ne saboda gudun magudi bayan da aka zargi wasu 'yan jam'iyyar da raba kayan zaben tun kafin masu ruwa da tsaki su yi taro kan zaben.

Soke zaben dai ya shafi sauran zabukan da jam'iyyar za ta gudanar a ranar alhamis da kuma juma'a.