Majalisar dokokin Najeriya ta hana jihohi karbo bashi

Harabar majalisar dokokin Najeriya

Majalisar dattawan Najeriya ta hana jihohi karbo bashi daga kasashen waje ba tare da ba da cikakken bayani kan aikin da za su yi da kudaden ba.

Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake samun karuwar jihohin da ke neman bashi daga kasashen waje.

Sai dai majalisar dattawan ta ce gwamnatin tarayya za ta iya karbo bashin dala biliyan daya da rabi daga kasashen waje domin gudanar da wasu ayyukan raya kasa.

Sanata Ahmed Muhammad shi ne mataimakin shugaban kwamatin harkokin kudi na majalisar, ya shaidawa BBC cewa sun hana jihohi karbar bashin ne ganin cewa ba sa bin ka'ida wajen kashe kudin.

Ya ce yawan karbar bashin zai sa jihohin su dauwama cikin bashi, abin da ya ce zai yi mummunan tasiri ga jama'a.