'Mu muka kai harin bama-bamai a Jos - Boko Haram

Rikicin Jos
Image caption Mutane tamanin sun rasa rayukansu a Jos

Kungiyar Jama'atu Ahlussuna liddawati wal jihad wadda aka fi sani da boko haram, ta yi ikirarin ita ce ta kai hare-haren nan na bama-bamai da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na internet, kungiyar ta ce ta kai harin ne domin nuna rashin jin dadinta ga rashin adalcin da tace ana yi wa Musulmi a Jihar Plateau da ma Najeriya baki daya.

Mai yiwuwa wannan ya zo wa wasu mutane da mamaki, ganin cewa kungiyar a baya tana kai hare-hare ne a jihohin Borno da Bauchi, sai kuma ga shi suna ikirarin bulla jihar Plateau.

Sai dai akwai wadanda suke kokwanton wannan ikirarin da kungiyar ta yi, suna ganin kungiyar ta dauki nauyin kai harin ne kawai don neman suna.

Tuni dai hukumomin 'yan sanda suka nuna shakku a kan ikirarin kungiyar.

Shafin Intanet

Wani shafin intanet mai suna mansoorah.net ne ya wallafa ikirarin na kungiyar Jama'atu Ahlussuna liddawati wal jihad wacce aka fi sani da suna Bokom Haram, inda take cewa ita ce ta kai hare-haren na ranar juma’a da ta gabata, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama kuma suka janyo wani tashin hankali na ramuwar gayya.

Kungiyar ta Boko Haram dai a cewar shafin na Intanet, ta bayyana cewa ta kai hare-haren ne domin taimakawa wa musulmai kubuta daga abinda ta kira rashin adalci da ake nuna musu a jihar Pilato da ma Najeriya baki daya.

A jiya kwamishinan 'yan sandan jihar ta Pilato ya musanta cewa kungiyar Bokmo haram ce ta kai hare-haren bama-baman, inda ya danganta lamarin da siyasa.

Shi kansa gwamnann jihar Jonah Jang ya bayyana cewa ba masu kishin addini ne suka kai hare-haren ba, hasali ma ‘yan siyasa ne masu son haddasa rigima tsakanin musulmi da kirista a jihar ke da hannu a tashin bama-baman.

Mutane da dama dai na nuna shakku kan ikirarin na Boko Haram cewa su ne suka kai hare-haren bama-baman, amma dai wasu na ganin akwai yiwuwar gaskiya a ikirarin kungiyar.

Kungiyar ta Boko Haram dai ta fi kai hare-hare ne a Jihohin arewa maso gabas na Najeriya, musammam Bauchi da Borno

Kawo yanzu dai alkaluma daga hukumar agajin gaggawa ta Najeriya na cewa kimanin mutane tamanin ne suka rasa rayukansu a tashin bama-baman da kuma tarzomar da ta biyo baya, yayinda wasu kimanin dari biyu kuma suka jikkata.

'Satar Shanu'

A wani lamarin dake da nasaba da wannan kuma, Kungiyar Miyetti Allah ta Fulani makiyaya ta bayyan cewa an sace shanu sama da dari uku na mambobinta, yayinda aka gano gawawwakin wasu kimanin arba’in a karamar hukumar Jos ta Kudu ta jihar Plateau.

Sakataren Kungiyar Miyetti Allah na kasa, Saleh Bayeri ya ce suna kan cigiyar shanun tare da hadin gwuiwar jami’an tsaro a jihar.

Kawo yanzu dai ana ci gaba da samun lafawar al’amura a garin na Jos da kewaye, inda aka dade ana fuskantar yawan tashe-tashen hankula na kabilanci da na addini, amma dai mutane na ci gaba da kasancewa cikin fargaba.