Mutane 173 aka kashe a Ivory Coast

Mutane 173 aka kashe a Ivory Coast - MDD
Image caption Dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke baiwa Ouattara kariya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaben kasar Ivory Coast, sun yi asarar mutuwar mutane 173.

Wannan kiyasi na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da matsin lamba kan Laurent Gbagbo da ya sauka daga kan karagar mulki.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana duba yiwuwar karkafa dakarunta da ke kasar, inda sojojin kasar ke arangama da magoya bayan Alassane Ouattara.

Duka Majalisar ta Dinkin Duniya da kuma manyan kasashen duniya sun ce Alassane Ouattara ne ya lashe zaben.

Hukumar kare hakkin bil'adama wacce ke tattaunawa a birnin Geneva kan lamarin. Ta ce mutane 173 aka kashe a makon da ya gabata, yayin da aka kama wasu 500.

Wakilin BBC Thomas Fessy a birnin Abidjan, ya ce akwai rahotannin hare-hare kan magoya bayan Mr Ouattara, amma sojojin da ke goyan bayan Gbagbo sun hana a binciki abinda ke faruwa.

Magoya bayan Ouattara sun nemi Kotun Duniya mai hukunta laifukan yaki, ta binciki laifukan da magoya bayan Gbagbo suka aikata.

Mr Ouattara da magoya bayansa na zaune a wani otel a birnin Abidjan, inda sojojin Majalisar Dinkin Duniya 800 ke ba su kariya.