Cuba na wallafa bayanan da Wikileaks ya bankado

Tutar kasar Cuba
Image caption Cuba na wallafa bayanan Wikileaks

Kasar Cuba ta fara fassara da kuma wallafa takardun sirrin da shafin internet na wikileaks mai kwarmata bayanai ya fitar kan Amurka.

Tuni dai takardun sirrin suka fara bayyana a wani shafin internet na kasar Cuba.

Takardun dai sun yi magana kan rashin lafiyar tsohon shugaban kasar Fidel Castro, abin da kuma wani sirri ne da gwamnatin kasar ba ta son a yi magana akai.

Gwamnatin ta Cuba ta ce tana wallafa bayanan ne don nunawa duniya irin mulkin kama-karyar kasar Amurka.