An kwace asusun ajiyar kudin Ivory Coast daga hannun Gbagbo

Mista Laurent Gbagbo, shugaban Ivory Coast
Image caption Ministocin kudi sun hana Gbagbo juya akalar asusun kasar

Ministocin ma'aikatun kudi na kasashen yammacin Afirka sun yanke shawarar mikawa Alasanne Ouattara, mutumin da ya lashe zaben kasar asusun ajiyar kudin kasar da ke babban bankin yankin.

Hakan zai yi nakasu sosai ga gwamnatin Mista Laurent Gbagbo, wanda gwamnatinsa ke samun rabin kudaden gudanarwarta daga bankin.

Ministocin sun yanke shawarar ne a matsayin wani shiri na kwace mulki daga hannun Mista Gbagbo.

Har yanzu dai Mista Gbagbo ne ke juya akalar kafafen yada labarai, da kuma rundunar sojin kasar, sai dai tunda an hana bashi kudi daga babban bankin yankin, zai yi wuya ya iya biyan sojojin albashin watan gobe.

Matakin da ministocin ma'aikatun kudin suka dauka na cike da hatsari, kasancewa Ivory Coast na taka muhimmiyar rawa a yankin sakamakon kudaden da ta ke samu daga cinikin koko.

Nan gaba kadan ne a yau shugabanin kasashen nahiyar za su yi taro a Najeriya kan rikicin kasar.