Nijar ta samu albarkatun noma bayan fari

A shekarar da ta gabata a jamhuriyar Nijar, ba a samu saukar ruwan sama da wuri ba, kuma ruwan ya dauke kafin nunar amfanin gona.

Hakan ya jefa al'umar kasar sama da Miliyan bakwai cikin halin ukuba sakamakon yunwar da mutanen suka sha fama da ita.

Kananan yara da dama ne suka rasa rayukansu sakamakon tamowa a wancan lokacin, yayinda miliyoyin dabbobi suka mutu sakamakon yunwa.

Gwamnatin kasar ta Nijar da taimakon kasashen duniya da kungiyoyi masu hannu da shuni sun kawo wa mutanen dauki ta hanyar sayar da abinci a farashi mai rahusa a wuraren da ke da matsakaiciyar matsalar yunwa, yayinda aka raba shi kyauta a wuraren da aka gano matsananciyar matsalar.

An samu damuna mai albarka daga baya

"Masu iya magana na cewa shekara ba ta gadon shekara, Allah ya saukar da Rahamarsa a wannan damunar, manoman Nijar sun dara." A cewar babban daraktan ma'aikatar gona ta jihar Maradi Mallam Jika Abubakar.

Ya ce; "Damuna ta yi kyau a duk fadin kasar ta Nijar."

Kasashe kamar su Jamus sun taimaka da irin shuka ingantacce domin baiwa manoman kasar ta Nijar damar samun albarkatun gona isasshe kuma cikin lokaci.

Ita ma a nata bangaren, gwamnatin kasar ta yi kira ga manoman da su dage ga noman iri.

Kamar jihar Maradi ana iya cewa sauran jihohin ma sun dara a wannan shekara. A wani gari Jiratawa da ake kira gidan mace daya da wakiliyar BBC Cima Illa Issoufou ta ziyarta, ta tarar da garin ya rude da 'kibin dawo' abinda ba kowanne gida ake daka wa ba a waccan shekarar saboda rashin aukinsa.

Al'mubazzaranci

A garin Sawon Nasarawa kuwa, wakiliyar BBC ta yi kicibis da wani bikin zanen suna. Mai bikin ya shaida mata cewa an yi haihuwar tun lokacin damuna, rashin abinci ya sa aka dage bikin sai a ranar.

Mai bikin ma ya yi dan nasa bidiri nan shi ma bayan da ya kade sama da dame 15 ya kautar da dama ga maroka.

Wata matsala da yanzu haka mazauna karkara suka fara kokawa a kai ita ce ta yadda 'yan uwa da abokan arziki na birane ke zuwa karbe musu dan abincin da suka noma.

Ita dai wannan al'ada da ake kira tsuntsuwa, mutanen birnin ne dake da 'yan uwa a karkara da zarar kaka ta yi, sai su sayi dan gishiri da daddawa wani lokacin ma har da dan sabulu da matattun tufafi, su je su kai musu, sai a ga adda ta a bani zanzaro.

Mutanen kauyen kuma sukan tattaro musu hatsi, wani lokacinma mutun guda kan iya samun sama da buhu biyar.

Farashin kayan abinci

A garin Tasawa, wakiliyar BBC ta yi hira da sarkin noma Alh Hamza Tsamiyar Kura wanda ya jadada mata kyawu damunar. Sai dai ya koka da yadda manoma ke kai abincinsu kasuwa suna sayar wa. A cewarsa gwamnati ce ya dace ta saye a kan farashi nagari.

Shi ma wani manomi Ali Auta ya bayana wa BBC cewa, sun samu albarkar noma sai rokon da su ke ga gwamnati ta sayi amfanin gonar tasu da daraja.

Dan jin yanda farashin abincin yake, Wakiliyar BBC ta shiga kasuwar Cizon Kurege inda ta tattauna da mallam Abdulnassiru wanda ya bayyana mata cewa manoma na dari-dari wajen sayar da abincin ganin matsalar da suka fi fama da ita.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin gwamnatin kasar ta Nijar kan ko akwai niyar sayen abincin ga manoma dan basu damar sayara wa a farashi mai rahusa, sai dai Mallam Jika Aboubakar ya shaida wa BBC cewa sun rubuta wa magabatansu kan wannan batu kuma suna jiran amsa nan da wani dan lokaci.

Yayinda wasu yankunan ke murna har ma suka fara al'mubazzaranci da abinci, wasu yankunan har yanzu sun zuba ido ne suna jiran sa'ida.

Wannan matsalar rashin samun albarkatun gona gare su bana, tana da nasaba da matsalar ambaliyar ruwan da suka yi fama da shi.

Tuni dai masu nazari kan sha'anin noma suka fara hasashen cewa da zarar gwamnatin kasar ta Nijar ta dage wajen karfafawa manyan manoman kasar kan noman ingantaccen iri matsalar karancin abinci ko yunwa za su zamo tarihi a kasar ta Jamhuriyar Nijar.