Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ghana ta fara hako danyen man fetur

Image caption Ghana ta bi sahun kasashen Afrika da ke da arzikin danyen man fetur

A kasar Ghana a ranan 15 ga watan Disamba ne shugaban kasar John Atta mills ya kaddamar da aikin fara fitar da danyen man Fetur a babban birnin jihar Yammacin kasar wato Takoradi.

An gudanar da bukukuwan ne tare da shirya wata kasaitacen hawan daba na sarakuna da al'umomin kasar a sansanin mayakan sama na kasar dake birnin.

Cikin wadanda suka halarci bukukuwan har da tsofaffin shugabannin kasar guda biyu watau Jerry Rawlings da John Kufuor.

Wakilin BBC a Ghana Iddi Ali, wanda shi ma ya halarci bikin dabar ya hada mana wannan rahoto na musamman.