Yan Somaliya 12 na fuskantar tuhumar ta'addanci a Holland

An kama wasu Yan Somalia 12 a tashar jiragen ruwa ta Rotterdam a Kasar Holland a kan zargin kasancewa da hannu a aikace aikacen ta'addanci.

Masu gabatar da kara a Rotterdam sunce bayanai daga hukumar leken asiri ta kasar ta Holland sun nuna cewar 'yan Somalia da yawa na shirin kai wani hari a kasar ta Holland, kusan nan bada jimawa ba.Kamar dai yadda Shugaban masu gabatar da karar, Gerrit Van der Burg ya fada: Ya ce, "da ranar juma'a ne muka samu bayani daga hukumar leken asiri cewar akwai yiwuwar kai harin ta'addanci nan bada dadewa ba, kuma yan Somalia da yawa za su iya kasancewa da hannu."

An dai bincike wani shagon sayar da tarho da gidaje 4 da kuma dakuna biyu na otel, amma kuma ba a samu makamai ko kuma nakiyoyi ba.

Shedu sunce masu bincike sun dauki hotuna.