Woodgate da Kean za su bar Tottenham

Harry Rehknapp
Image caption Harry Rehknapp ya nace cewa Luka Modric ba zai je ko'ina ba

Akwai yiwuwar Jonathan Woodgate da Robbie Keane su bar kungiyar Tottenham saboda dalilai daban-daban.

Shi dai Jonathan Woodgate ana saran koci Harry Redknapp zai ba da shi aro ne zuwa wata kungiyar saboda ya murmure daga raunin da yake fama da shi.

"Zan so na yi haka domin na ba shi damar buga wasu wasanni," a cewar Redknapp.

Robbie Keane ma ana saran zai bar kulob din, bayanda Redknapp ya ce dan wasan mai shekaru 30 ya kosa da zaman benci.

Amma kocin ya ce dan tsakiya Luka Modric wanda aka ce Chelsea na zawarci, ba zai je ko'ina ba.