Mahimmancin bikin Kirsimeti ga kiristoci

A lokacin da Kiristoci a duniya ke bukin Kirsimati domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Isa, Alaihi Salam ko kuma Yesu Kiristi, Fafaroma Benedict ya bayyana fatan samun zaman lafiya a yankunan dake fama da tashe tashen hankula, hade kuwa da yankin gabas ta tsakiya.

A cikin jawabinsa na murnar Kirsimati wanda ya gabatar daga saman wata Baranda a Basilicar St Peter a fadar Vatican, ya ce yana fatan karamar Kirsimati ta sake bayyana a kasar da aka haifi Yesu almasihui, ta kuma taimaka wa 'yan Isra'ila da Palasdinawa wajen samun zaman lafiya da lumana.

Haka kuma Fafaroman ya bukaci samun dauwamammen zaman lafiya a Ivory Coast da Somalia da kuma Sudan.

Ya kuma bayyana goyon baya ga Kiristoci 'yan tsiraru da ake gallazamawa a Iraqi da China da kuma ga mutanen da ke murmurewa daga bala'o'i a Haiti da kuma yankin Latin Amurka.

Ranar Kirsimati dai rana ce da mabiya addinin kirista ke gudanar da bukukuwa da yin ibada da addu'o'i da kuma ziyarar juna domin nuna godiya ga mahalicci.

To ko akwai abubuwa na musamman da malaman addinin kiristar ke nunawa mabiyansu a daidai wannan lokaci? .

Pastor Dokta James Mobel Wuye dan kungiyar tuntuba tsakanin musulmi da mabiya addinin kirista ne; " Asali idan Kirista na kwarai ne, ya tuna da mutuwar Isa almasihu mai cetonsa, kuma a yi masa godiya. Wasu da dama na kuma tafiya ne domin ganin, 'yan uwansu, domin tattauna al'ummaran rayuwa da kuma yadda za su ci gaba". "Ana kuma raye-raye da wake-wake da kuma cin abinci domin tunawa da ranar."

"Muna kuma kira da mutane da su guji mugayen ayyuka a lokacin, domin lokaci ne na tuba da kuma ibada." In ji pasto Wuye.

Abubuwan da kirista ke mayar da hankali a kai

Tun kafin zuwan ranar kirsimeti dai, kirista kan mayar da hankali wajen kintsawa domin tunkarar wannan rana. A ganin Pastor Danjuma Alkali Bom na ikilisiyar ECWA dake Lemu Road Kaduna, gyara zuciya da kuma zumunci su ne ya kamata a yi; " Ya kumata muna wannan murna ta hanyar ziyartar 'yan uwa domin nuna farin cikin mu".

"Kamata ya yi, mu kaunaci juna domin Yesu ya ce ka kaunaci makiyinka kamar kanka, idan yana cikin matsala ka taimake shi."

"Muna kuma biyayya ga shugabanni, saboda samun ci gaba a kasa, idan lokacin rajista ya yi muna kira ga sauran 'yan uwa da su zabi wanda za su taimaki rayuwarsu." In ji Pastor Danjuma

Bayanai na nuna cewa lokacin kirsimeti, lokaci ne na gabatar da addu'o'i ga madaukaki baya ga bukukuwa na nuna jin dadi.

To ko a wannan karon wadanne addu'o'i malaman addini suka maida hankali a kai? Rabaran Ibrahim Sanusi shi ne sakataren kungiyar CAN na karamar hukumar Soba jihar Kaduna; "Muna maida hankali ne kan adu'oi domin samar da zaman lafiya a kasa."

"Muna kira ga Kirista da su guji neman abun duniya domin samun ci gaba."

Lokacin kirsimeti dai, lokaci ne da malaman addini kan mika sako ga mabiya domin inganta kyawun zamantakewa da kwanciyar hankali. Rabaran Father Raymond Nandand, wakilin Bishop-Bishop na jihar Kaduna a kungiyar CAN, ya shaida min irin sakonnin da akan mika ga mabiya.

"Ranar ce ta albarka, bai kamata mutane su daura wa kansu abin da Allah bai daura musu ba. Su bar ma Allah komai, domin shi kadai zai magance musu matsalolinsu". In ji Father Raymond. Ganin yadda kirsimetin wannan shekarar yaci karo da kankamar harkokin siyasa, Rev John Joseph Hyab na kungiyar CAN ta Kaduna ya yi karin bayani; " Yesu ne babban shugabanmu, idan za mu zabi shugabannin, mu zabi wadanda za su kyautata rayuwar mu. Kada mu zabi wadanda za su raba kawunan mu".

"Muna ci gaba da adu'a ga Allah ya bamu Shugaba na gari a wannan biki na krisimeti, wanda ba zai nuna banbancin addinin ko kabila ba." Mabiya addinin kirista a Najeriya da sauran kasashen duniya, a yanzu na nan na gudanar da bukukuwan kirsimeti, tare da gabatar da adduo'i'n samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da yalwa da kuma fatan Allah zai maimata ganin wannan rana.