Bamai-bamai sun kashe mutane 32 a Jos

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya ce Gwamnatinsa za ta yi dukanin abunda za ta iya domin gurfanar da wadanda suka tayar da bama bamai jiya a Birnin Jos.

Hukumomi dai sunce mutane 32 ne aka kashe sannan wasu fiye da 70 suka samu raunuka a jerin fashe fashen.

An tsaurara matakan tsaro a yankin wanda yake tsaka -tsakin yankin arewaci da yake da galibin musulmi da kuma kudanci mai Kiristoci.

Kwamandan rundunar tsaro na hadin guiwa Birgediya Janar Hassan Umar, ya ce jami'an tsaro na ci gaba da sintiri a yankunan da wannan al'amari ya abku inda suke umurtar mazauna yankin da su koma gidajen su.

A yau da safe ma dai an ji karar bindigogi a wasu unguwannin birnin na Jos.

Jihar Filato dai ta dade tana fama da tashe-tashen hankula na kabilanci dana addini dakan janyo hasarar dimbin rayuka da dukiya.

Hari a Maiduguri

Mutane shida ne aka ba da rahoton sun rasa rayukansu a garin Maiduguri da ke arewacin Najeriya lokacin da wadansu 'yan bindiga suka kai hari kan wata majami'a.

Haka nan kuma an ba da rahoton cewa mai gadin wata majami'ar daban ya rasa ransa, yayinda sojoji masu tabbatar da tsaro suka samu nasarar dakile hari na uku a kan wata majami'ar.

Wadannan hare-hare dai sun auku ne a jajibirin Kirsimeti a garin na Maiduguri wanda ya sha fama da tashe-tashen hankulan da ake alakanta su da 'yan kungiyar Boko Haram.