Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Dogaro da kai tsakanin nakasassu

Image caption Jama'a da dama ne ke shiga harkokin barece-barace

A Najeriya rashin samun kulawar hukumomi ga nakasassu da tsofaffi marasa galihu na daga abubuwan dake haddasa yawace-yawacen bara da irin wadannan rukuni na al'umma ke yi.

Sau tari sukan ce suna yin hakan ne domin kulawa da rayuwarsu kamar sauran jama'a, a wasu lokutan ma ba su tsaya ga kan su ba kawai harma da wasu da ke tallafa musu a yawan barar.

Saidai kuma ba duka aka taru aka zama daya ba domin kuwa akwai wasu daga cikin irin wadannan mutane masu rauni cikin al'umma da suka gwammace su rike wata sana'a don dogaro da kai maimakon bara ko zaman jiran wani tallafi daga hukuma.

Wakilinmu a jihar Jigawa dake Najeriya Muhammad Annur Muhammad ya hada mana rahoto a kan wannan batu: