Helikwabtocin yaki na Pakistan sun kashe yan gwagwarmaya arba'in

Jami'ai a Pakistan sunce jirage masu saukar angulun yaki dauke da bindigogin atilere sun kashe masu tayar da kayar baya 40 a yankin kabilu na Mohmand dake arewa maso yammaci a kusa da kan iyaka da Afghanistan.

Hakan ya zo ne kwana biyu bayan kashe yan gwagwarmaya da yawa da kuma sosjoji 11 a lokacin da aka kai hari a kan wani wurin tsaro a yankin.

Labarin kai harin ramuwar gayyar da helikwabta ya zo ne yan sa'o'i kawai bayan wani dan kunar bakin wake sanye da lullubin mata na burqa ya kai hari a wani babban taron mutanen da aka raba da gidajensu a gundumar Bajaur mai makwabtaka.

Mutane akalla 40 ne dai aka kashe sannan wasu 60 suka samu raunuka, yayinda suke jiran taimakon abincin MDD.