Tawagar shugabannin Afirka za ta Ivory Coast

Wasu daga cikin shugabannin kasashen ECOWAS
Image caption Wasu daga cikin shugabannin kasashen ECOWAS

Wata tawagar shugabannin kasashen Afirka ta yamma za ta je kasar Ivory Coast jibi Talata, a kokarin shawo kan Shugaba Laurent Gbagbo ya sauka daga mulki.

Shekaranjiya ne dai Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, ta yi barazanar daukar matakin soja idan Mista Gbagbon ya ki sauka.

Sai dai wani kakakin gwamnatin Mista Gbagbon,Yao Gnamiein, ya ce daukar matakin soja zai kara dagula al'amurra ne, ya kuma sa rayukan miliyoyin baki 'yan kasashen waje da ke zaune a kasar cikin hadari.

"Majalisar Dinkin Duniya ba za ta yi amfani da karfi a kan shugaban kasa ba.

"Tarayyar Afrika ma ba za ta yi amfani da karfi a kan shugaban kasarmu ba.

"Ya kamata su fahimci musabbanin takaddamar", inji Mista Gnamiein. A wurare da dama dai ana daukar Alassane Ouattara a matsayin wanda yayi nasara a zaben shugaban kasar.