Tashin hankali ya kara rincabewa a Jos.

Wani jami'in tsaro a Jos, jihar Plato, Nijeriya
Image caption Wani jami'in tsaro a Jos, jihar Plato, Nijeriya

Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato a Nijeriya na cewa yau al'amurra sun kara rincabewa inda aka sami hasarar rayuka da dukiya sakamakon wani sabon tashin hankali.

Tashin hankalin dai ya biyo bayan tashin wasu bama-bamai ne a ranar Juma'a da ta gabata, inda mutane da dama suka rasa rayukansu, kuma tashin hankalin na yau ya hada da kone-kone, da kuma harbe-harbe na bindigogi.

Jami'an tsaro na ci gaba da sintiti a unguwanni na dama na birnin na Jos.

Jihar Filato dai ta dade tana fama da rigingimu na kabilanci da na addini, da suka yi sanadiyar mutuwar dubban mutane cikin kimanin shekaru goma.