Shugabanni zasu lallashi Gbagbo ya sauka

A yanzu haka dai an fahimci cewa wata tawagar shugabannin kasashen Afrika ta yamma zata je kasar Kotde Vuwa jibi Talata, a kokarin shawo kan shugaba Laurent Gbagbo da ya sauka daga mulki.

Shekaranjiya ne kungiyar kasashen yammacin Afrikar, ECOWAS ta yi barazanar daukar matakin soja idan Mr Gbagbon ya ki sauka.

Sai dai wani kakakin gwamnatin Mr Gbagbon,Yao Gnamiein, ya ce daukar matakin soja zai kara dagula al'amurra ne, ya kuma sa rayukan miliyoyin baki 'yan kaasshen waje dake zaune a kasar cikin hadari.

A wurare da dama dai ana daukar Alassane Ouattara ne a matsayin wanda yayi nasara a zaben shugaban kasar.