Pira ministan Kenya zai shiga tsakani a Cote D'Ivoire

Sojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a Abidjan
Image caption Sojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a Abidjan

Tarayyar Afrika ta nemi Pira ministan Kenya Raila Odinga da ya jagoranci yunkurin da take yi na kawo karshen rikicin siyasar da ake fama da shi a Cote D'Ivoire ko Ivory Coast.

Shugaban Hukumar Tarayyar Afrika, Jean Ping ya ce ya nemi Mr Odinga da ya taka muhimmiyar rawa wajen warware rikicin, wanda ya samo asali daga nacewar da shugaba mai ci Laurent Gbagbo ya yi cewa ba zai mika mulki ga mutumin da duniya ta amince cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a watan jiya, watau Alassane Outtara.

Mr Odinga ya ce zai yi iya kokarinsa.

Ya kuma ce "Mr Gbagbo ya sha fada cewa shi mai bin tafarkin Demokradiyya ne, saboda haka ne ma ya shafe shekaru da dama yana gudun hijira a Faransa. Saboda haka zan yi kokarin nuna masa cewa lokaci ya yi da zai bada kyakyawan misali. "

Tun da farko sai da magoya bayan Alassane Outtara suka mamaye cikin ruwan sanyi ginin ofishin jakadancin Cote D'Ivoire a birnin Paris na Faransa.

Hakan ya biyo bayan matakin da Faransan ta dauka ne na amincewa da wakilin Mr Ouattara a matsayin halaltaccen jakadan Cote D'Ivoire a kasar ta Faransa, wadda ita ta yiwa Cote D'Ivoire din mulikin mallaka.

Wani kakakin magoya bayan Mr Ouattara din ya ce ba su lalata komai ba; illa sun cire hoton Laurent Gbagbo dake rataye a jikin bangon ofishin.

An shirya ranar Talata, Mr Gbagbon zai gana da wakilan kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, wadda ita ma ta nemi Mr Gbagbo da ya sauka daga mulki.

A ranar Litinin dai al'ummar kasar ta Cote D'Ivoire ba su saurari kiran da aka yi musu ba na shiga yajin aikin gama gari da nufin kawo karshen abun da ya hana ruwa a gudu a takaddamar da ake yi dangane da zaben shugaban kasa na watan jiya.

Jam'iyyun siyasa masu goyon bayan Alassan Ouatata ne, suka kira yajin aikin a wani yunkuri na tilastawa shugaba mai ci Laurent Gbagbo sauka daga karagar mulki.

Sai dai wakilin BBC ya ce an yi ta hada-hada a yankunan birnin Abidjan wadanda suka jefawa Mr Ouattara kuri'a.

Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO dai ta gargadi Mr Gbagbo cewa mai yiwa ta dauki matakan soja a kansa, idan bai sauka daga kan karagar mulki ba.