Muhimman al'amura a Najeriya a 2010

Marigayi Umaru 'Yar'aduwa
Image caption Marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa

Kwanci-tashi shekarar 2010 ta zo karshe; kuma a cikin wannan shekara abubuwa da dama ne suka auku ta fuskar siyasa da tattalin arziki da zamantakewa da dai sauransu.

Shekarar ta 2010 dai ta shigo ne a daidai lokacin da ake ganiyar cece-ku-ce dangane da batun rashin lafiyar shugaban Najeriya na lokacin, Alhaji Umaru Musa 'Yar’aduwa.

'Yan Najeriya da dama sun yi ta bayyana damuwa a kan abin da suka kira rashin sanin inda shugaban kasar yake, da kuma takamaiman halin da yake ciki.

Sai dai kurar waccan cece-ku-ce ta lafa, kai har ma jita-jitar da ake ta yayatawa a wancan lokacin cewa Shugaba Umaru Musa 'Yar’aduwan ya rasu ta kau, bayan da Sashen Hausa na BBC ya yi hira da shi ta wayar tarho daga inda yake jinya a Asibitin Sarki Faisal da ke birnin Jidda.

Mansur Liman, wanda ya gudanar da hirar, ya nemi jin ko wanne sako shugaban kasar ke da shi ga 'yan Najeriya.

Shugaban ya amsa da cewa:

"'Yan uwa na 'yan Najeriya, ina so in sanar da ku cewa ina kan samun sauki insha-Allahu; ".

A cikin watan Fabrairun shekarar ne kuma Majalisar Dokoki ta Kasa ta yanke shawarar bayar da rikon ragamar mulkin Najeriya ga mataimakin shugaban kasa, Dokta Goodluck Jonathan, har ya zuwa lokacin da shugaban kasar zai sami lafiya ya koma kan mukaminsa.

Bayan da Dokta Goodluck Jonathan ya zama mukaddashin shugaban kasa, ya kaddamar da sauye-sauyen mukamai na ministoci, kuma ya umarci shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Maurice Iwu, ya tafi hutun share fagen barin aiki.

Image caption Jana'izar marigayi Shugaba Umaru 'Yar'aduwa

Wani muhimmin abu da ya auku a shekarar ta 2010, wanda ya girgiza zukata kuma ya jefa jama'a cikin alhini, shi ne rasuwar Shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa.

An kuma yi jana'izar marigayin ne a birnin Katsina mahaifarsa.

Rasuwar shugaban kasar ta kawo sauye-sauye da dama a fagen siyasar Najeriya.

Muhimmi kuma daga cikinsu shi ne mataimakinsa, Dokta Goodluck Jonathan, ya maye

gurbinsa.

Sannan daga bisani aka nada tsohon gwamnan jihar Kaduna, Architect Muhammad Namadi Sambo, a matsayin mataimakin sabon shugaban Najeriyar.

Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

A cikin shekara ta 2010 din ne kuma, Shugaba Goodluck Jonathan ya nada Farfesa Attahiru Jega a matsayin sabon shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), bayan da aka sauke Farfesa Maurice Iwu, wanda aka yi ta cece-ku-ce game da ci gaba da zamansa a wannan mukami.

Batun tsarin karba-karbar mulki, wanda jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta kirkiro wa kanta, shi ma wani muhimmin al'amari ne da ya ya bullo da wani sabon salo, tare da zazzafar cece-ku-ce a tsakanin kusoshin jam'iyyar da ma sauran 'yan Najeriya da dama a cikin shekarar.

A shekarar ta 2010, Najeriya ta yi fama da rikice-rikice iri-iri a wurare daban-daban, ciki kuwa har da zauren Majalisar Wakilai ta tarayya, inda wasu 'yan majalisar suka ba hammata iska.

Takaddama ta kaure ne a lokacin da Chile Igbawua ya nemi gabatar da wani batu wanda 'yan majalisar da ke yunkurin tsige kakakin Majalisar, Honourable Dimeji Bankole, suka zaci kudirin dakatar da su ne.

Image caption Kakakin Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dimeji Bankole

Nan take sai shugabansu, Dino Melaye, ya tashi yana kokarin gabatar da nasa kudirin; daga nan sai hayaniya ta kaure.

Sakamkon wannan damben ne kuma aka raunata Honourable Doris Uboh, da Honourable Solomon Awhinawi, wanda ya samu karaya a hannu.

'Yan majalisar da aka dakatar dai—Dino Melaye, da Ehiogie West-Idahosa, da Independence Ogunewe, da Solomon Awhinawi, da Austin Nwachukwu, da Abba Anas, da Gbenga Oduwaiye, da Kayode Amusan, da Gbenga Onigbogi, da Bitrus Kaze, da Doris Uboh—sun garzaya kotu a kan wannan batu.

Daga baya-bayan nan kuma hukuncin da kotun ta yanke ya bayar da umarnin a sake mayar da su kan kujerunsu na majalisar.

Haka nan kuma rikicin da ake dangantawa da addini da kabilanci, ya yi ta jeka ka

dawo a Jos, babban birnin Jihar Filato, cikin shekarar da ake bankwana da ita.

Rikicin dai ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.

Ga kuma abin da wani mazaunin birnin na Jos ya shaida wa wakilin BBC dangane da yadda halin rayuwa ya kasance a lokutan ire-ren wadancan rikice-rikice:

"Gaskiya rayuwa ta kasance cikin zullumi, da fargaba, da kunci; mun rasa dukiyoyi da rayuka masu yawa.

"sannan ba halin walwala--sama da sati mutum yana gida bai je ko ina batakurar ta kai takura".

Ba a gama kashe wutar rikicin na Jos ba, sai kwatsam rikicin Boko Haram ya sake kunno kai a jihohin Borno da Yobe da kuma Bauci na shiyyar arewa maso

gabashin Najeriya.

Image caption Wani daga cikin ofisoshin 'yansanda da ake zargin 'yan Boko Haram da lalatawa

Wasu mazauna birnin Maiduguri sun yiwa wakiliyar BBC bayani dangane da hare-haren da ake zargin 'yan kungiyar ta Boko Haram, wadanda ke kiran kansu Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad, ne suka rika kai wa:

"Babur sabo kal suka zo da shi suka yi fakin; kuma akwai mota daya wadda ta zo ta tsaya.

"Da [wanda ke cikin motar] ya fara harbi, sai sauran ma suka shigo ta baya...ba zan iya [tantance yawansu] ba, amma wadanda suke harbi, ga uku ga biyu—biyar [ke nan] wadanda na gani".

"...Bayan sun gama harbin sai suka zubar da kayan suka buga babur dinsu suka gudu".

A cikin wannan shekara mai ficewa dai, an gamu da bala'in gobara a kasuwannin

wasu sassan Najeriya, wanda ya yi sanadiyyar asarar miliyoyin kudade da kadarori

masu dimbin yawa, har ma da asarar rayuka a wadansu kasuwannin.

Kasuwar Kantin Kwari da ke Kanon Dabo na cikin wuraren da al'amarin ya shafa.

Wakilin BBC ya ruwaito cewa wutar ta shafe sama da sa'o'i goma tana ci a kasuwar ta Kantin Kwari, inda ta kone rumfuna sama da dubu da daya da kuma kayayyakin biliyoyin nairori.

Baya ga gobara, ambaliyar ruwa ma ta shafi sassa da dama na Najeriya a cikin

shekarar ta 2010.

Image caption Ambaliyar ruwa a Jihar Jigawa

Hakan kuma ya yi sanadiyyar salwantar gidaje da dabbobi da kayan abinci da sauran kadarori masu yawan gaske.

A wasu wuraren ma har da asarar rayukan jama'a.

Haka nan kuma an yi fama da annobar kwalara, galibi a arewacin Najeriya, inda aka bayar da rahoton rasa rayukan mutane da dama.

Sha'anin tsaro ya gamu da babban kalubale a Najeriya a cikin shekarar ta 2010.

Matsalar fashi da makami da sace mutane ana garkuwa da su don neman fansa da sauran miyagun laifuffuka sun karu musamman ma a shiyyar kudu maso gabashin kasar.

Matsalar sace mutane ana garkuwa da su dai, wadda ta shafi attajirai da 'yan kasuwa da manyan ma'aikatan gwamnati da 'yan siyasa da shugabannin addini da 'yan boko da dai sauransu, ta kai kololuwa ne a watan Yulin shekarar, yayin da aka sace wasu 'yan jarida su hudu a jihar Abiya.

Alhaji Hafizu Ringim, wanda a lokacin shi ne Mataimakin Sufeto Janar na 'yansandan Najeriya mai kula da shiyya ta tara, ya fayyace girman matsalar da kuma irin kokarin da jami'an tsaro suka rika yi don kubutar da 'yan jaridar da aka sace:

"Tura ta kai bango...don haka tilas ne a tashi tsaye, ko ba don komai ba saboda 'yan jarida...kakatunsu da hargowarsu sun tayarwa da shugabannin kasar na hankali, ya tayarwa da shugabannin 'yansanda hankali; kai har kananan 'yansanda ma ya tayar masu da hankali.

"Don haka ya wajaba mu yi dukkan abin da ya kama a yi...akwai wadannan Turawan da na'urorinsu wadanda za su iya nuna mana hanya, inda ake tsammani wadannan mutane da aka cafke da kuma wadanda suka cafke su su ke".

Daga bisani dai an samu nasarar kubutar da 'yan jaridar lami lafiya.

Sai dai kuma sha'anin tsaron ya sake yin tuntube da wani cikas a watan Satumba, bayan da aka sace wasu yara 'yan makaranta su goma sha biyar, a kan hanyarsu ta zuwa makaranta a birnin Aba na jihar Abiya.

Al'amarin dai ya tilasta rufe bankuna da kasuwanni, kuma harkokin kasuwanci da sauran al'amuran yau da kullum sun tsaya cik a wannan birni na tsawon kwanaki.

An dai sami nasarar kubutar da wadancan yara 'yan makaranta, kuma bayanai sun ce sha'anin tsaro ya inganta a yankin, sakamakon tura rundunar sintiri ta hadin gwiwa da aka yi.

Har ila yau dai, sha'anin tsaro ya gamu da karin kalubale a gidan yarin garinBauchi a cikin wannan shekara mai ban-kwana, inda wadansu mutane da ake zargin 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad ne suka balle gidan

yarin.

Image caption Bayan tashin bama-bamai a Abuja

A ranar daya ga watan Oktoban shekarar ta 2010 ne kuma Najeriya ta

cika shekaru hamsin cif da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na

Birtaniya.

An kuma shirya bukukuwa na musamman a jihohi talatin da shida na

kasar gami da birnin tarayya Abuja.

Sai dai kuma bikin ya gamu da abin kaico sakamakon fashewar wasu abubuwa

da ake zargin bama-bamai ne a harabar dandalin da ake bikin.

Wani wanda ya ganewa idonsa aukuwar lamarin ya yi karin bayani:

"Mun ji wata kara ne na fashewar wani abu kamar bindiga kamar kuma wata nakiya wadda ake kokarin fasa ta ba ta fashe ba da kyau...wannan abu ya faru a tsakiyar 'yansanda, bayan shi Shugaban Kasa ya wuce ke nan, ya kuma dandamalin da ya ke tsaye...".

Tun kafin tashin wadannan abubuwa dai, kungiyar nan mai ikirarin kwato 'yancin yankin Naija Delta, wato MEND, ta rarrabawa kafofin yada labarai wata sanarwa, wadda a cikinta ta yi gargadin cewa a cikin 'yan mintuna bama-bamai za su tashi a harabar da ake bikin da kuma wajensa.

Image caption Masu ta da kayar baya a yankin Naija Delta

A yayin da shekarar ta 2010 ke bankwana kuma, kwatsam sai aka ji bullar wani hari, wanda ake hangen an yi bankwana da jin irinsa a yankin Naija Delta mai albarkatun man fetur.

Wakilin BBC ya ruwaito cewa an kai harin ne a kan bututan mai mallakar kamfanonin Chevron da Agip a Jihar Delta.

Wata kungiya mai suna Niger Delta Liberation Force a karkashin jagorancin John Togo ce ta dauki alhakin kai harin.

Image caption Wani wanda ya ji rauni a rikicin Jos a watan Maris

Wannan hari dai daga baya-bayan nan ya yi sanadiyyar rufe matatun mai na

Fatakwal da Warri da kuma Kaduna, sakamakon lalacewar bututun da ke tura masu

danyen man da suke tacewa.

Haka nan kuma a ranar jajiberin bikin Kirsimeti an sami aukuwar fashewar wasu

abubuwa a garin Jos na jihar Filato.

Rahotanni kuma sun ce al'amarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin talatin da biyu, wasu da dama kuma sun jikkata.

A bangare wasan kwallon kafa kuwa, masu lura da harkokin wasanni sun ce Najeriya

Image caption 'Yan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles

ta ga rashi, ta kuma ga samu a shekarar ta 2010.

Chima Dozie Nwatu, wani dan wasa kuma mai sharhi a kan harkar wasan kwallon kafa, ya kuma yi karin bayani game da haka:

"Ban yarda cewa kungiyar wasan kwallon kafa ta Super Eagles za ta fita waje wasa a kabar da ita haka kawai ba.

"Ai ka ga yadda karawarsu ta kasance da Argentina a Afirka ta Kudu.

"Ina ganin muhimmin abu a nan shi ne a rika yin shirye-shiryen da suka dace a kan kari, domin muna da 'yan wasa gwanayen taka leda a kasar nan".

Sai dai kuma Chima Dozie Nwatu yana ganin kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasa

ta taka rawar gani:

"Ai ka ga yadda suka taka kwallo a gasar kwallon mata 'yan kasa da shekaru ashirin ta duniya da aka yi kwanan nan.

"’Yan matan sun kokarta, kuma su ne suka fidda mu kunya a idon duniya".

Duk da wannan fadi-tashi da aka yi ta fama da shi a Najeriya a cikin shekara ta 2010, Farfesa Balarabe Sani Garko na Asibitin Koyarwa na Jami'ar

Image caption Wani mai fama dacutar kwalara a Jihar Borno

Ahmadu Bello da ke Shika-Zariya, yana ganin an samu ci gaba a kasar ta fuskar kiwon lafiya:

"...Gwamnatin tarayya ta yi alkawari tun kafin wannan shekarar cewa za a samu cibiyoyi na kula da lafiya wadanda suka kware a bangarori uku na Najeriya; Zariya tana ciki kuma mun fara gani a kasa, saboda akwai bita da ake tura wadansu ma'aikatan lafiya su je su koyo, misali tiyata a kan zuciya.

"Akwai kuma shirin gwamnatin tarayya na inshorar lafiya, wato asusun gata.

"Sai kuma bangaren riga-kafi: ciwon polio yanzu ina ganin saura kiris in ma bai tafi gaba daya ba daga Najeriya".

Dangane da cutar kwalara kuma, Farfesa Balarabe cewa ya yi rashin tsafta ne ya kawo ta kuma wajibi a fadakar da mutane su rika wanke hannu bayan sun fito daga ba-haya.

To, ko yaya shekarar mai ban kwana ta kasance ga jama'a daidaiku a Najeriya?

Hassan Haruna: "Gaskiya harkar kasuwanci a shekarar 2010 ba magana, saboda ba ciniki; manya-manya ma wadanda mu ke sayen kaya a hannunsu kuka su ke yi".

Danladi Hugu: "Ni manomi ne; gaskiya shekarar 2010 mu ta zo mana da alheri, don ta fi 2009.

"Mun samu alheri, amfanin gona gaskiya ba laifi: mun samu hatsi—dawa, wake, ridi—duk mun samu".

Abdul Aziz Aliyu: "Wannan shekara ta 2010 sai dai mu ce mun godewa Allah tun da dai har na yi aure, na sayi babur ina acaba...."

A yanzu dai shekara ta 2010 ta fi, ta bar 'yan Najeriya da kyakkyawan fatan Allah Ya sa bana ta fi bara kyau.