Amurka da Jamus sun koka kan hukunta Khodorkovsky

Mikhail Khodorkovsky
Image caption Magoya bayansa sun ce shariar na da nasaba da siyasa

Kasashen Amurka da Jamus sun bayyana damuwa, bayan da wata kotu a Mosko ta sami attajirin nan na Rasha, Mikhail Khodorkovsky da laifin almundahana da halalta kudaden haram.

Mr Khodorkovsky, wanda a da shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a Rasha, kuma babban abokin hamayyar Vladimir Putin, kotun ta same shi da laifin sace man fetur din da darajarsa ta kai dala biliyan 27 da kuma halalta kudaden cinikin man.

Wakilin BBC ya ce Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hillary Clinton ta ce hukuncin ya sa alamar tambaya kan yadda 'yan siyasa suke tsoma baki a harkar sharia a Rasha.

Shi kuwa ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle, bayyana shariar ya yi da cewa wani koma baya ne ga Rasha.

Tun dai a shekara ta 2005 ne ake tsare da shi a kurkuku bisa laifin kaucewa biyan haraji, amma daga baya an zarge shi tare da wani abokin huldarsa Platon Lebedev, da laifin sace sama da ton miliyon dari 2 na man fetur daga kamfaninsu na Yukos, tare da halalta kudaden da suka sayer da man.

Hukumomi sun kama da dama daga cikin magoya bayansu yayinda suke zanga-zangar nuna adawa da shariar a wajen kotun.

Lawyan Mr Khodorkovsky, Yuriy Shmidt, ya ce shariar tana da nasaba da siyasa, kuma za su daukaka kara.