Sanyi ya dakatar da sufuri a Amurka

Dusar kankara a New York
Image caption Dusar kankara a New York

Matsanancin sanyin hunturu na kawo matukar cikas ga zirga-zirga a yankunan da ke kusa da gabar teku a Amurka.

An soke sauka da tashin dubban jiragen sama a filin jirgin sama na New York, an kuma rufe babban filin jirgin sama na J.F. Kennedy.

An kuma soke sauka da tashin daruruwan jiragen sama jiya Lahadi wadnda suka hada da jiragen kamfanonin British Airways da Virgin Atlantic wadanda ke zuwa daga wadansu kasashen da kuma wadanda ke tashi daga arewaci zuwa gabashin Amurka.

Hakazalika, kamfanin jiragen kasa na Amtrak ya dakatar da daukar fasinjoji daga New York zuwa Boston, inda ake tsammanin samun dusar kankarar da zurfinta ya wuce santimita talatin.

An kuma yi shelar dokar ta baci a wadansu manyan jihohi hudu da suka hada da Maryland, da North Carolina da Virginia da kuma New Jersey.