Wenger ya yi murna da samun nasara

Arsene Wenger
Image caption Manajan Arsenal Arsene Wenger

Manajan kulab din Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana cewa nasarar da suka yi ta cin Chelsea uku da daya ta kara musu kwarin gwiwa a gasar pirimiya

Wannan ne karon farko da kulab din Arsenal ya samu nasara a kan Chelsea a jerin wasanni shida, kuma wannan nasarar ce ta ba su damar zama na biyu a teburin gasar, inda suka rufa wa Manchester United baya.

A shekara ta 2008 ne Arsenal ta doke Chelsea.

Da wannan nasarar baya-bayan nan da Arsenal ta samu a kan Chelsea, Chealsea ta koma ta hudu a teburin gasar pirimiya, lamarin da ke sanya manajan kulub din fuskantar karin matsin-lamba.