Iran ta rataye Siadat

Shugaban Iran Ahmadinajad
Image caption Shugaban Iran Ahmadinajad

Kasar Iran ta rataye mutumin da ta samu da aikata laifin yi wa Hukumar Mossad ta Isra`ila leken asiri.

Kamafanin dillancin labaran kasar Iran, Irna ta ba da labarin cewa kasar Iran ta rataye wani mutum bayan ta same shi da aikata laifin yin aikin leken asiri ga hukumar Mossad ta kasar Isra`ila.

Jami`an ma`aikatar shari`ar kasar dai sun bayyana cewa an rataye Ali Akbar Siadat, wanda dan asalin kasar Iran ne a cikin gidan yarin Evin da ke Tehran.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya ruwaito cewa Ali Akbar Siadat ya kwashe shekaru masu yawa yana yin leken asiri wa hukumar asiri ta Mossad ta kasar Isra`ila, kuma ya ba da bayanan da suka shafi ayyukan Sojin kasar Iran.

A shekara ta 2008 ne aka tsare shi tare da matarsa lokacin da ya yi kokarin barin kasar.

Siadat, a cewar kamfanin dillancin labarai na Irna, ya tabbatar da cewa ya tura wa hukumar Mossad wasu bayanai game da ayyukan sojojin Iran, kuma an biya dala dubu sittin sakamakon ba da bayanai na musamman ga gwamnatin kasar Isra`ila.

A karkashin dokar kasar Iran dai akan yi hukuncin kisa ne ga masu aikata laifin leken asiri.