Tawagar kashedin karshe ta isa kasar Ivory Coast

Laurent Gbagbo
Image caption Laurent Gbagbo ya yi zaman dirshan

Shugabannin kasashen Afirka ta yamma sun fara isa kasar Ivory Coast don tattaunawa a kan rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da ke cike da takaddama.

Shugabannin, wadanda suka fito daga kasashen Saliyo da Benin da Cape Verde za su bai wa Laurent Gbagbo ne dama ta karshe domin ya sauka daga karagar mulkin kasar Ivory Coast cikin girma da arziki.

Shi dai Mr Gbagbo ya nace kan cewa shi ne ya ci zabe.

Ya ki mika ragamar mulki ga Alassane Ouattara, mutumin da kasashen duniya suka yi amanna cewar shi ne ya lashe zaben.

Majalisar tsarin mulkin kasar ce ta soke nasarar da Alassane Ouattara ya samu a zaben da aka yi ranar 28 ga watan Nuwamban da ya wuce ta hanyar kafa hujja da cewar an yi magudi a arewacin kasar, majalisar da wani na hannun-daman Gbagbo yake shugabanta.

Kakakin gwamnatin kasar Saliyo ya shai da wa BBC cewa tawagar shugabannin kasashe na kungiyar tattalin arzikin afirka ta yamma, ECOWAS za su bai wa Mr Gbagbo ne damar sauka daga kujerar mulki ne ba tare da an ci masa muntunci ba.