Shari`ar Khodorkovsky: Rasha ta yi raddi ga kasashen yamma

Mikhail Khodorkovsky
Image caption Magoya bayansa sun ce shariar na da nasaba da siyasa

Rasha ta zargi kasashen yamacin duniya da kokarin yi mata matsin-lamba da ta ce ba za ta yadda da shi ba game da shari`ar da ake yi wa dan kasuwar man da ake tsare da shi, Mikhail Khodorkovsky.

Ma`aikatar harkokin wajen kasar Rasha ce ta yi wannan zargin lokacin da take mai da martani dangane da sukar da kasar Amurka da Jamus suka yi ranar Litinin din da ta wuce bayan an yanke wani hukunci na biyu na samun Khodorkovsky da laifi.

Shi dai Khodorkovsky, wanda a wani lokaci ya taba zama barazana ga tsohon shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin an yanke masa hukuncin yin almubazaranci ne.

A shekara ta 2005 ne aka fara tsare shi bisa aikata almundahana da kin biyan haraji.

Khodorkovsky da shi da abokin kasuwancinsa Platon Lebedev sun halarci zaman kotun na ranar Talatar da ta gabata, lokacin da alkali ke jera laifukan da kotun ta ce ta samu Khodorkovky da aikatawa.

Babu wani bayani a kan lokacin da kotun za ta fadi tsawon daurin da za a yi musu.

Cikin wata sanarwar da ta sanya a shafinta na internet, Ma`aikatar harkokin wajen Rasha ta ce ba za ta taba sauraron duk wani matsin-lamba ba.

"Muna so kowa a gida da kasshen waje ya ji da harkokin gabansa.

Ma`aikatar ta bayyana zargin da aka yi cewa ana hukuncin ganin dama a Rasha da cewar marar tushe ne.

Tun a shekara ta 2003 ake tsare da Khodorkovsky, kuma kasa da shekara kenan da kammala zaman gidan yari sakamakon hukuncin da aka yi masa na farko bisa aikata almundahana.

A jiya ne dai, kasashen Amurka da Jamus suka bayyana damuwa, bayan da wata kotu a Mosko ta sami attajirin na Rasha, Mikhail Khodorkovsky da laifin almundahana da halalta kudaden haram.

Mr Khodorkovsky, wanda a da shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a Rasha, kuma babban abokin hamayyar Vladimir Putin, kotun ta same shi da laifin sace man fetur din da darajarsa ta kai dala biliyan 27 da kuma halalta kudaden cinikin man.

Wakilin BBC ya ce Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hillary Clinton ta ce hukuncin ya sa alamar tambaya kan yadda 'yan siyasa suke tsoma baki a harkar sharia a Rasha.

Shi kuwa ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle, bayyana shariar ya yi da cewa wani koma baya ne ga Rasha.

Hukumomi sun kama da dama daga cikin magoya bayansu yayinda suke zanga-zangar nuna adawa da shariar a wajen kotun.

Lawyan Mr Khodorkovsky, Yuriy Shmidt, ya ce shariar tana da nasaba da siyasa, kuma za su daukaka kara.