Ni zan fara amincewa da 'yancin kudancin Sudan - al-Bashir

Taswirar kasar kudancin Sudan da ake son kirkiro wa
Image caption Taswirar kasar kudancin Sudan da ake son kirkiro wa

Shugaban kasar Sudan, Omar al-Bashir ya ce zai kasance na farko da zai dauki kudancin Sudan a matsayin kasa mai cin gashin kanta muddin hakan ta samu a zaben referendum da za a yi a ranar 9 ga watan Janairu mai kamawa.

Mr. Bashir ya fadawa dubban magoya bayansa a wani gangami da suka yi cewa za su a rungumi kudancin Sudan a matsayin 'yar uwa.

Yace: "Mun shaida wa 'yan uwanmu na kudanci cewa wuka da nama na hannunku, idan kuna san hadin kai kofa a bude take."

Ya ce Khartoum zata taimaka wa jama'ar kudancin Sudan din wajen gina kasarsu, kamar yadda suke san ganin an samu tsaro da kwanciyar hankali a yankin.