Matsalar cin hanci ta yi kamari a China

Yaki da cin hanci a kasar China
Image caption Kasar China

Gwamnatin kasar China ta ci alwashin daukar kwararan matakai, wajen yaki da cin hanci domin samun amincewar jama'ar kasar.

A rahotansu na farko kan batun, mahukuntan China sun tabbatar da cewa matsalar cin hanci da rashawa ta yi kamari a kasar, wanda ya hada da makudan kudade da kuma abubuwan da suka saba doka.

Wani jami'i a gwamnatin Chinan yace an sa mu karuwar laifukan da suka shafi cin hanci da dama a duk fadin kasar.

A cikin rahotan, gwamnatin ta ci alwashin rage irin makudan kudaden da ake kashewa jam'iyyun siyasa da kuma a tarurrukan da ake a kasar.