Shugabannin ECOWAS za su koma Ivory Coast

Laurent Gbagbo
Image caption Laurent Gbagbo ya yi zaman dirshan

Shugabannin kasashen Afirka ukun da suka gana da shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo, domin shaida masa bukatar ya sauka daga mulki, salin alin ko kuma a tsige shi ta karfin tsiya, za su sake komawa kasar a mako mai zuwa.

Daukar wannan matakin ya biyo bayan ganawar da shugabannin suka yi ne da shugaban Najeriya Goodluck Jonatahan wanda shi ke rike da shugabancin kungiyar ta ECOWAS.

Shugabannin uku da suka hada da na Benin, Saliyo da Cape Verde sun gana da Mr. Gbagbo ne a madadin kungiyar ECOWAS, wadda ke daukar Alassane Ouatara a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi kwananan a kasar.

Shugaba Goodluck Jonatahan na Najeriya ya shaida wa manema labarai cewa "Shugabannin sun dawo ne domin kawo muin rahoto, amma za su koma ranar 3 ga watan Janairu."

Shugaba Goodluck Jonathan ya kuma kara da cewa: "Ana ci gaba da tattauna wa, a don haka ne za su koma."

Sai dai a gefe daya manyan hafsoshin kasashen ECOWAS din sun gudanar da taro a Abujar domin tsara irin matakin sojan da za a dauka a kan Ivory Coast, matukar tattauanwar da ake yi ta ci tura.

Ministan sadarwa na kasar Saliyo Ibrahim Ben Kargbo ya ce Tilas ne a ba Mr. Ouatara damar jan ragamar Ivory Coast kuma Laurent Gbagbo ya yarda da zabin jama'a.

Shugaban kasar Benin Boni Yayi ya ce ganawar ta yi armashi, amma bai yi wani karin bayani ba.

Shi dai Mr Gbagbo ya nace kan cewa shi ne ya lashe zaben da ake takaddama a kai.

Majalisar tsarin mulkin kasar ce ta soke nasarar da Alassane Ouattara ya samu a zaben da aka yi ranar 28 ga watan Nuwamban da ya wuce ta hanyar kafa hujja da cewar an yi magudi a arewacin kasar, majalisar da wani na hannun-daman Gbagbo yake shugabanta.

Kakakin gwamnatin kasar Saliyo ya shai da wa BBC cewa tawagar shugabannin kasashe na kungiyar tattalin arzikin afirka ta yamma, ECOWAS za su bai wa Mr Gbagbo ne damar sauka daga kujerar mulki ne ba tare da an ci masa muntunci ba.