Matsayin kasashen Larabawa kan Sudan

Amr Moussa a  Kartoum babban birnin kasar Sudan
Image caption Amr Moussa a Sudan

Sakatare janar na kungiyar kasashen Larabawa Amr Moussa, ya yi alkawarin cewa kungiyarsa za ta ci gaba da taimaka wa kudancin Sudan, ko da kuwa ya balle daga arewacin kasar.

Mr Moussa na magana ne a Juba, bayan tattaunawarsa da shugaban kudancin Sudan din Salva Kiir, inda ya ba su kyautar dakunan shan magani na tafi da gidanka goma.

A ranar 9 ga watan Janiru ne za a yi zaben raba gardama game da baiwa kudancin Sudan din 'yan cin kai.

Mr. Moussa ya gana da shugabannin Sudan a Khartoum ranar Talata, inda yace bai ga wata alamar cewa arewaci ko kudancin Sudan na san komawa cikin yaki ba.